1
أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ (ثَلاَثَاً) اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلاَمُ, وَمِنْكَ السَّلاَمُ, تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالْإِكْرَامِ
Ina neman gafarar Allah (3) Ya Ubangiji kai ne Aminci kuma daga gareka amincin ya ke, ka daukaka ya Ma'abocin girma da daukaka,
Majiya: Muslim 1/414.
2
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ, لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ [ثلاثاً], اللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ, وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ, وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الجَدُّ
Babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kadai kuma bashi da abokin tarayya kuma godiya ta tabbata a gare shi, kuma shi mai iko ne akan komai( 3) Ya Ubangiji babu mai hana abinda ka bayar kuma babu wata amfanarwa da wanda yake da girma yake yi daga girmanka.
Majiya: Al-Bukhari 1/255, Muslim 1/414.
3
لَا إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ, لَهُ الْمُلْكُ, وَلَهُ الْحَمدُ, وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ, لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ, وَلاَ نَعْبُدُ إِلاَّ إِيَّاهُ, لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الْفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ, لَا إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الكَافِرُونَ
Babu wani Ubangiji da sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya mulki naka ne kuma godiya ta tabbata a gareka kuma kai mai iko ne akan komai, babu tsimi kuma babu dabara sai na Allah babu wawani ubangiji sai Allah kuma kuma shi kadai muke bautawa, ni'ama tasa ce haka falala kuma shi ne wanda kyakkyawan yabo ya tabbata a gare shi, Babu wani Ubangi sai Allah muna masu tsarkake shi kuma Addini nasa ne koda kafirai sunki kuwa
Majiya: Muslim 1/415.
4
سُبْحَانَ اللَّهِ, وَالْحَمْدُ لِلَّهِ, وَاللَّهُ أَكْبَرُ (ثلاثاً وثلاثين) لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ, لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Subhanallahi walhamdu lillah wallahu Akbar (33) kuam babu wani abin bauta sai Allah shi kadai wanda bashi abokin tarayya, Mulki nasa ne haka kuma godiya, kuma Mai iko ne akan komai
Majiya: Muslim 1/418.
5
بسم الله الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ* اللَّهُ الصَّمَدُ* لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ* وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ﴾
بسم الله الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ* مِن شَرِّ مَا خَلَقَ* وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ* وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ* وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ﴾
بسم الله الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ* مَلِكِ النَّاسِ* إِلَهِ النَّاسِ* مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ* الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ* مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ﴾
(بَعْدَ كُلِّ صَلاَةٍ)
Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci." "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata." "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba." "Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi." Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya" "Daga sharrin abin da Ya halitta." "Da sharrin dare, idan ya yi duhu." "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle." "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada." Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne." "Mamallakin mutane." "Abin bautãwar mutãne." "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa." "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane." "Daga aljannu da mutane."
Majiya: Al-Ikhlas:1-4, Al-Falaq:1-5, An-Nas:1-6.
6
اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ (عَقِبَ كلِّ صَلاَةٍ)
Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
Majiya: An-Nasa'i (Hadith no. 100), Ibn As-Sunni (Hadith no. 121,Sahihul-Jami' As-Saghir 5/339, Silsilatul al-Ahadith as-Sahihah 2/697.
7
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ, لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Babu wani Ubangiji Sai Allah shi kadai kuma bashio da Abokin tarayya, kuma gareshi godiya take kuma yana rayawa kuma yana kashewa kuma shi ,ai iko ne akan komai Sau goma bayan Sallar Magriba da kuma Asuba
Majiya: At-Tirmizi 5/515, Ahmad 4/227, Zadul-Ma'ad 1/300.
8
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْماً نافِعاً, وَرِزْقاً طَيِّباً, وَعَمَلاً مُتَقَبَّلاً (بعد السلام من صلاة الفجر)
Ya Ubangiji ina rokonka Ilimi mai amfani da kuma Arziki mai tsafta da aiki karbabbe
Majiya: Ibn Majah, Sahih Ibn Majah 1/152, Majma' az-Zawaid 10/111.