1
اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاء وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ
Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
Majiya: Al-Hakim 1 / 562, Sahih at-Targhib wa at-Tarhib 1/273, at-Tabarani.
2
بسم الله الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ* اللَّهُ الصَّمَدُ* لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ* وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ﴾.
بسم الله الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ* مِن شَرِّ مَا خَلَقَ* وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ* وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ* وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ﴾.
بسم الله الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ* مَلِكِ النَّاسِ* إِلَهِ النَّاسِ* مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ* الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ* مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ﴾
(ثلاث مرات )
Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci." "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata." "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba." "Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi." Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya" "Daga sharrin abin da Ya halitta." "Da sharrin dare, idan ya yi duhu." "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle." "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada." Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne." "Mamallakin mutane." "Abin bautãwar mutãne." "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa." "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane." "Daga aljannu da mutane."
Majiya: Al-Ikhlas:1-4. Al-Falaq:1-5. An-Nas:1-6, Abu Dawud 4/322, At-Tirmizi 5/567, Sahih At-Tirmizi 3/182.
3 AI
أَمسينَا وَأَمسى الْمُلْكُ لِلَّهِ, وَالْحَمْدُ لِلَّهِ, لاَ إِلَهَ إلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ, لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ, رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذَه الْليلة وَخَيرَ مَا بَعْدَها, وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذَه الْليلة وَشَرِّ مَا بَعْدَها, رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ وَسُوءِ الْكِبَرِ, رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِي النَّارِ وَعَذَابٍ فِي الْقَبْرِ
Mun shiga maraice alhali mulki ya tabbata ga Allah; godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai ne, ba shi da abokin tarayya; gare Shi mulki yake kuma gare Shi godiya take, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kome. Ya Ubangijina, ina rokonka alherin wannan dare da alherin abin da ke bayansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrin wannan dare da sharrin abin da ke bayansa. Ya Ubangijina, ina neman tsarinka daga ragwanci da mummunan tsufa. Ya Ubangijina, ina neman tsarinka daga azaba a cikin wuta da azaba a cikin kabari.
Majiya: Muslim 4/2088.
4
اللَّهُمَّ بِكَ أَمسينا, وَبِكَ أَصبحنا, وَبِكَ نَحْيَا, وَبِكَ نَمُوتُ وَإِلَيْكَ المصيرُ
Ya Ubangiji dakai muka wayi gari kuma dakai mukayi yammaci, kuma dakai muke Rayuwa kuma dakai muka mutuwa kuma gareka muke tashi
Majiya: Sahih At-Tirmizi 3/142.
5
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ, خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ, وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ, أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ, أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ, وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنوبَ إِلاَّ أَنْتَ
Ya Ubangiji kaine ubangiji na babu wani Ubangiji sai kai kai ka halicce ni kuma ni bawanka ne kuma ina nan akan alkaarinka gwargwadon iko ina neman tsarinka daga abinda nayi kuma ina furuci da ni'amar da kayi mun kuma ina furuci da zunubaina kayi mun gafara babu mai gafarta zunubai sai kai kadai
Majiya: Al-Bukhari 7/150, An-Nasa'i, At-Tirmizi.
6 AI
اللَّهُمَّ إِنِّي أَمسيتُ أُشْهِدُكَ, وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ, وَمَلاَئِكَتَكَ, وَجَمِيعَ خَلْقِكَ, أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ, وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَرَسُولُكَ (أربع مرات)
Ya Allah, na shiga maraice ina shaidar ka, da masu ɗaukar Al-Arshinka, da mala'ikunka, da dukan halittunka, cewa kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai, kai kaɗai ne, ba ka da abokin tarayya, kuma cewa Muhammadu bawanka ne kuma manzonka. (Sau huɗu.)
Majiya: Abu Dawud 4/317, An-Nasa'i, Ibn As-Sunni.
7 AI
اللَّهُمَّ مَا أَمسى بِي مِنْ نِعْمَةٍ أَوْ بِأَحَدٍ مِنْ خَلْقِكَ فَمِنْكَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ, فَلَكَ الْحَمْدُ وَلَكَ الشُّكْرُ
Ya Allah, duk wata ni'ima da na samu a wannan maraice, ni ko wani daga halittunka, daga gare ka kaɗai take, ba ka da abokin tarayya; saboda haka gare ka godiya take kuma gare ka shukura take.
Majiya: Abu Dawud 4/318, Ibn As-Sunni (Hadith no. 41), Ibn Hibban (Hadith no. 2361).
8
اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَدَنِي, اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي, اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي, لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكُفْرِ, وَالفَقْرِ, وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ, لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ (ثلاث مرات)
Ya Ubangiji ka bani lafiya a jikina Ya Ubangiji ka bani lafiya cikin jina ya Ubangiji ka bani lafiya cikin gani na Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga Kafirci da kuma talauci, kuma ina neman tsarin ka daga Azabar kabari babu wani ubangiji sai kai ( Sau uku )
Majiya: Abu Dawud 4/324, Ahmad 5/42, An-Nasa'i, Ibn As-Sunni (Hadith no. 69), Ibn Hibban (Hadith no. 2361).
9
حَسْبِيَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيهِ تَوَكَّلتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ (سبع مرات)
Allah ya ishe ni Babu wani Ubangiji sai shi gare shi na dogara kuma shi ne ubangijin Al'arshi mai girma ( Sau bakwai )
Majiya: Ibn As-Sunni (no. 71), Abu Dawud 4/321, Ibn As-Sunni.
10
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ, اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ: فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي, وَمَالِي, اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَاتِي, وَآمِنْ رَوْعَاتِي, اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَينِ يَدَيَّ, وَمِنْ خَلْفِي, وَعَنْ يَمِينِي, وَعَنْ شِمَالِي, وَمِنْ فَوْقِي, وَأَعُوذُ بِعَظَمَتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي
Ya Ubangiji ina rokonka afuwa da lafiya a Dauniya da lahira Ya Ubangiji ina rokonka afuwa da da lafiya, a cikin Acikin Duniya ta da Ahalina da Dukiya ta Ya Ubangiji ka Suturta Al'aura ta kuma ka amintar da ni abinda nake tsoro, Ya Ubangiji ka kiyaye ni a gabana da baya na, da dama na da haguna da sama na da kasa na kuma ina neman tsari da girmanka kada a hallaka ni ta karkashina
Majiya: Sahih Ibn Majah 2/332, Abu Dawud.
11
اللَّهُمَّ عَالِمَ الغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ, رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ, أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ, أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي, وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطانِ وَشَرَكِهِ, وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءاً, أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ
Ya Ubangiji Masanin fake da fili wanda ya halicci sama da kasa ubangijin komai kuma mai mulkinsu na shaida babu wani ubnagiji sai kai ina neman tsarinka daga sharrin kaina da sharrin shaidan da mataimakansa ko kuma inyi wani zunubi ko injawo shi ga wani Musulmi
Majiya: Sahih At-Tirmizi 3/142, Abu Dawud.
12
بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلاَ فِي السّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ (ثلاث مرات)
Da sunan Allah wanda babu abinda yake utarwa da fadin sunansa a cikin sama ne ko kuma a kasa kuma shi mai ji ne masani
Majiya: Abu Dawud 4/323, At-Tirmizi 5/465, Ibn Majah 2/332, Ahmad.
13
رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبَّاً, وَبِالْإِسْلاَمِ دِيناً, وَبِمُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم نَبِيّاً (ثلاث مرات )
Na yarda da Allah shi ne Ubangiji kuma Musulunci shi ne Addini kuma Annabi Muhammadu shi ne Annabi (Sau Uku)
Majiya: Ahmad 4/ 337, An-Nasa'i, Ibn As-Sunni (no. 68), At-Tirmizi 5/465.
14
يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ بِرَحْمَتِكَ أَسْتَغيثُ أَصْلِحْ لِي شَأْنِيَ كُلَّهُ وَلاَ تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ
Ya rayayye tsayyae da kansa ina neman agajinka da rahamarka ka inganta mun al'amura na baki daya kuma kada ka barni da kaina ko daidai da kiftawar Ido
Majiya: Al-Hakim 1/545.
15
أَمسينَا وَأَمسى الْمُلْكُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ, اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذَه الْليلة:فَتْحَها, وَنَصْرَها, وَنورَها, وَبَرَكَتَها, وَهُدَاها, وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِيها وَشَرِّ مَا بَعْدَها
Mun wayi gari kuma mulki yana hannun Allah Ina rokonka Alkairin wannan rana budinta da Nasararta da haskenta da albarkarta da kuma shiriyarta, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin duk abinda yake cikin ta da sharrin abinda yake bayanta
Majiya: Abu Dawud 4/322.
16 AI
أَمسينا عَلَى فِطْرَةِ الْإِسْلاَمِ, وَعَلَى كَلِمَةِ الْإِخْلاَصِ, وَعَلَى دِينِ نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم, وَعَلَى مِلَّةِ أَبِينَا إِبْرَاهِيمَ, حَنِيفاً مُسْلِماً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشرِكِينَ
Mun shiga maraice a kan fiɗirar Musulunci, a kan kalmar tsarki, a kan addinin Annabinmu Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da kuma a kan al'adar babanmu Ibrahim, mai karkata zuwa ga gaskiya, mai miƙa wuya, kuma bai kasance daga masu shirka ba.
Majiya: Ahmad 3/406-7, 5/123, An-Nasa'i, At-Tirmizi 4/209.
17
سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ (مائة مرة)
Tsarki ya tabbata ga Allah da kuma godiya ( Sau dari )
Majiya: Muslim 4/2071.
18
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ, لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ, وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ (عشر مرات أو مرة واحدة عند الكسل)
Babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah shi kadai wanda bashi da Abokin tarayya Mulki nasa ne haka ma godiya kuma shi mai Iko ne akan komai ( Sau goma) ko ( Sau daya in ya gaji)
Majiya: An-Nasa'i, Abu Dawud 4/319, Ibn Majah, Ahmad 4/60.
19
أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ (مائة مرة في اليوم)
Ina neman gafarar Allah kuma ina tuba izuwa gare shi ( Sau dai)
Majiya: Al-Bukhari, Muslim 4/2075.
20
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ (ثلاث مرات)
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta
Majiya: Ahmad 2/ 290, An-Nasa'i, At-Tirmizi 3/187, Ibn As-Sunni (Hadith no. 68), Ibn Majah 2/266.
21
اللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلِّمْ عَلَى نَبَيِّنَا مُحَمَّدٍ (عشر مرات)
Yace: Allah kayi salati da tsira ga Anabinmu Muhammad ( Sau goma )
Majiya: At-Tabrani, Sahih at-Targhib wa at-Tarhib 1/273.