يَبْدَأُ بِرِجْلِهِ الْيُمْنَى, وَيَقُولُ: أَعُوذُ بِاللَّهِ العَظِيمِ, وَبِوَجْهِهِ الْكَرِيمِ, وَسُلْطَانِهِ الْقَدِيمِ, مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ. [بِسْمِ اللَّهِ, وَالصَّلَاةُ] [وَالسَّلَامُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ] اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ
Zai fara gabatar da kafarsa ta dama ne a lokacin shiga, sannan ya ce Ma'ana: ina neman tsarin Allah mai girma, da fuskarsa mai alfarma, da na mulkin sa dadadde daga shaitan la'ananne. Ma’ana: Da sunan Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah. Ya Allah ka bude mini kofofin rahmarka.
Majiya: Abu Dawud, Sahihul-Jami' As-Saghir (Hadith no. 4591), Ibn As-Sunni (Hadith no. 88), Abu Dawud 1/126, Sahihul-Jami' 1/528, Muslim 1/494, Ibn Majah 1/128-129.