1
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا, وَرَزَقَنِيهِ, مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da ni wannan kuma ya azurta ni shi ba tare da wata dabara ba, kuma ba da karfi ba.
Majiya: At-Tirmizi, Abu Dawud, Ibn Majah.
2
الْحَمْدُ لِلَّهِ حَمْداً كَثِيراً طَيِّباً مُبَارَكاً فِيهِ, غَيْرَ [مَكْفِيٍّ وَلاَ ] مُوَدَّعٍ, وَلاَ مُسْتَغْنَىً عَنْهُ رَبَّنَا
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah godiya mai yawa tsarkakakka mecike da albarka a ciki ba ta da iyaka kuma ba yankewa, kuma ba mai barin Allah Ubangijin mu.
Majiya: Al-Bukhari 6/214, At-Tirmizi 5/507.