1
إِذَا أَكَلَ أَحَدُكُمْ طَعَاماً فَلْيَقُلْ بِسْمِ اللَّهِ, فَإِنْ نَسِيَ فِي أَوَّلِهِ فَلْيَقُلْ بسمِ اللَّهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ
Idan dayanku zai ci abinci to ya ce: Da sunan Allah idan kuma ya manta bai fada ba afarkon cin abincin to ya ce: Da sunan Allah Farko da karshe.
Majiya: Abu Dawud 3/347, At-Tirmizi 4/288.
2
مَنْ أَطْعَمَهُ اللَّهُ الطَّعَامَ فَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنَا خَيْراً مِنْهُ, وَمَنْ سَقَاهُ اللَّهُ لَبَناً فَلْيَقُلْ اللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنَا مِنْهُ
Duk wanda Allah ya ciyar da shi abin ci ko ya shayar da shito ya ce: Ya Allah Ubangiji! Ka sanya mana albarka a cikinsa kuma ka kara mana shi
Majiya: At-Tirmizi 5/506.