Noor
Hausa
Noor / Addu'a / Yabon Allah / Falalar yin salati ga Annabi

Falalar yin salati ga Annabi

Yabon Allah · addu'o'i 5

Falalar yin salati ga Annabi 0:00
Saurara
1

قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلاَةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْراً

Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:“Wanda ya yi salata daya agare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi”.

Majiya: Muslim 1/288.

2

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: لاَ تَجْعَلُوا قَبْرِي عِيداً وَصَلُّوا عَلَيَّ؛ فَإِنَّ صَلاَتَكُم تَبْلُغُنِي حَيْثُ كُنْتُمْ

Kuma Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko ina kuka kasance

Majiya: Abu Dawud 2/218, Ahmad 2/367.

3

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: الْبَخِيلُ مَنْ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba”.

Majiya: At-Tirmizi 5/551.

4

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: إِنَّ لِلَّهِ مَلاَئِكَةً سَيَّاحِينَ فِي الْأَرْضِ يُبَلِّغُونِي مِنْ أُمَّتِي السَّلاَمَ

Kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: ‘Allah yana da wadan su mala’iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al’umma ta’.

Majiya: An-Nasa'i, Al-Hakim 2/421.

5

(وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: مَا مِنْ أَحَدٍ يُسَلِّمُ عَلَيَّ إِلاَّ رَدَّ اللَّهُ عَلَيَّ رُوحِيَ حَتَّى أَرُدَّ عَلَيْهِ السَّلاَمَ

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa”.

Majiya: Abu Dawud (Hadith no. 2041).