قَالَ جَابرُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: كَانَ رسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يُعَلِّمُنَا الْاسْتِخَارَةَ فِي الْأُمُورِ كُلِّهَا كَمَا يُعَلِّمُنَا السُّورَةَ مِنَ الْقُرْآنِ, يَقُولُ: (إِذَا هَمَّ أَحَدُكُمْ بِالْأَمْرِ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ مِنْ غَيْرِ الْفَرِيضَةِ, ثُمَّ لْيَقُلْ: اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ, وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ, وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيمِ؛ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ, وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ, وَأَنْتَ عَلاَّمُ الغُيُوبِ, اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأمْرَ - وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي – أَوْ قَالَ: عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ - فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ, وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي – أَوْ قَالَ: عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ – فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ, ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ) وَمَا نَدِمَ مَنِ اسْتَخَارَ الْخَالِقَ, وَشَاوَرَ الْمَخْلُوقِينَ الْمُؤْمِنِينَ وَتَثَبَّتَ فِي أَمْرِهِ, فَقَدْ قَالَ اللَّهُ سبحانه وتعالى: ﴿وَشاوِرْهُمْ فِي الْأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ﴾
(Idan ɗayanku ya yi niyyar wani al'amari, sai ya yi raka'a biyu ban da farilla, sannan ya ce:) Ya Allah, ina neman zaɓin alheri daga gare ka da saninka, ina kuma neman ƙarfi da ikonka, ina rokonka daga falalarka mai girma; domin kai mai iko ne ni kuma ba ni da iko, kai ka sani ni kuma ban sani ba, kuma kai Masanin gaibu ne. Ya Allah, idan ka san cewa wannan al'amari — ya kuma ambaci bukatarsa — alheri ne a gare ni a addinina, da rayuwata, da ƙarshen al'amarina (ko ya ce: a duniyata da lahirata), to ka ƙaddara mini shi, ka sauƙaƙe mini shi, sannan ka sa albarka a cikinsa. Idan kuwa ka san cewa wannan al'amari sharri ne a gare ni a addinina, da rayuwata, da ƙarshen al'amarina, to ka kau da shi daga gare ni, ka kuma kau da ni daga gare shi, ka ƙaddara mini alheri duk inda yake, sannan ka sa in yarda da shi.
Majiya: Al-Bukhari 7/162, Al-'Imran 3:159.