Noor
Hausa
Noor / Addu'a / Sallah / Azkar na kiran sallah

Azkar na kiran sallah

Sallah · addu'o'i 5

Azkar na kiran sallah 0:00
Saurara
1

يَقُولُ مِثْلَ مَا يَقُولُ المُؤَذِّنُ إِلاَّ فِي (حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ وَحَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ) فَيقُولُ: (لاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ)

Ma'ana: Musulmi zai fadi dukkan abinda mai kiran ‎sallah ya ce, saidai idan mai kiran sallar ya ce: ‎

Majiya: Al-Bukhari 1/152, Muslim 1/288.

2

يَقُولُ: وَأَنَا أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ, رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبَّاً, وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولاً, وَبِالْإِسْلاَمِ دِينَاً. يَقُولُ ذَلِكَ عَقِبَ تَشَهُّدِ الْمُؤَذِّنِ.

Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini. Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Majiya: Muslim 1/290, Ibn Khuzaymah 1/220.

3

يُصَلِّي عَلَى النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم بَعْدَ فَرَاغِهِ مِنْ إِجَابَةِ الْمُؤَذِّنِ

Zaiyi Sati ga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi bayan ya gama bibiyar mai kiran Sallah

Majiya: Muslim 1/288

4

اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ, وَالصَّلاَةِ الْقَائِمَةِ, آتِ مُحَمَّداً الْوَسِيلَةَ وَالْفَضِيلَةَ, وَابْعَثْهُ مَقَامَاً مَحمُوداً الَّذِي وَعَدْتَهُ, [إِنَّكَ لَا تُخْلِفُ الْمِيعَادَ]

Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.

Majiya: Al-Bukhari 1/152, Al-Bayhaqi 1/410

5

يَدْعُو لِنَفسِهِ بَيْنَ الْأَذَانِ وَالْإِقَامَةِ فَإِنَّ الدُّعَاءَ حِينَئِذٍ لاَ يُرَدُّ

Yana Addu'a ga kansa tsakanin kiran Sallah da Iqama sabida Addu'a a wannan lokacin

Majiya: At-Tirmizi, Abu Dawud, Ahmad, Irwa' al-Ghalil 1/262